An Nemi A Hukunta Likitocin Da Suka Manta Da Almakashi A Cikin Wata Mata Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwarta


Wani dangi a Kano ya zargi Asibitin ‘Abubakar Imam Urology’ da sakaci bayan mutuwar wata matar aure a dangin mai suna Aishatu Umar, wacce ake zargin ta sha fama da matsanancin ciwon ciki na tsawon watanni bayan tiyatar da aka yi mata inda aka bar mata almakashi a cikin cikinta.

Wani ɗan uwanta, Abubakar Mohammed, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta inda ya ɗora hoton marigayiyar da kuma hoton na’urar haske da aka ɗauka wanda ya nuna almakashin da ake zargin an manta da shi a jikin matar bayan tiyatar.

  • Rukunin Ba Da Tallafin Jinya Na Sin Da Asibitin Nijar Sun Gudanar Da Aikin Jinya Kyauta
  • Barin Almakashin Tiyata Acikin Ciki: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Ma’aikatan Asibiti 3

Mohammed ya ce, Aishatu ta rasu da misalin karfe 1 na dare a ranar Litinin bayan ta sha fama da ciwon da ya daɗe yana damunta tun bayan tiyatar da aka yi mata a asibitin a watan Satumban 2025.

A cewarsa, matar wacce ƴar uwar matarsa ce, ta kamu ne da rashin lafiya a Kano, inda kuma aka kai ta cibiyar kula da cututtukan da suka shafi mafitsara don yi mata tiyata. Ya yi iƙirarin cewa, jim kaɗan bayan tiyatar, Aishatu Umar ta fara jin matsanancin ciwon ciki inda ta riƙa komawa asibitin akai-akai.

“Bayan tiyatar, ta sha fama da matsanancin ciwon ciki. Duk lokacin da ta koma asibitin, maganin rage raɗaɗi kawai suke bata,” in ji Mohammed.

Mohammed ya ƙara da cewa, kwana biyu kacal kafin mutuwarta aka gudanar da gwaje-gwajen lafiya wanda ya kai ga ɗaukar hoton na’urar haske, wanda ya nuna cewa an bar almakashi a cikin jikinta a lokacin tiyatar watan Satumba.

Ya ce, an fara shirye-shiryen yin tiyatar gyara, amma Aishatu ta mutu a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026, kafin a yi tiyatar.

Bayan zarge-zargen, Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan lamarin. A sanarwar da jami’ar watsa labarai na asibintin, Samira Suleiman ta sanya wa hannu ta bayyana cewa, gwamnatin Jihar Kano ta umarci a gudanar da bincike na musamman a kan lamarin ta kuma dakatar da wasu ma’aikata uku da suka gudanar da aikin nan take ta kuma miƙa ta’aziyya ga iyalai da al’umma a kan rasuwar matar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *