Gwamnati Ta Yaba Wa Saudiyya Kan Sakin Ƴan Nijeriya 3
Gwamnatin Nijeriya ta gode wa Masarautar Saudiyya bisa sakin ƴan Nijeriya uku da aka tsare a Jeddah tun watan Agustan 2025, bayan samunsu da laifin da daga baya aka gano cewa an ƙaƙabawa musu ne ba tare da saninsu ba. A wata sanarwa da mai bai wa Ministan Harkokin Waje shawara kan kafafen watsa labarai, Alkasim Abdulkadir, ya fitar a ranar Laraba, yans mai bayyana cewa an wanke su daga duk wani tuhuma bayan cikakken bincike.
Sanarwar ta ce wadanda aka kama su ne Abdulhamid Sadieq, Maryam Abdullahi da Bahijah Abdullahi, wadanda ake zargin an haɗa musu haramtattun kayayyaki ne ta hanyar makircin miyagun kungiyoyin da ke aiki a filin jirgin Mallam Aminu Kano ba tare da sanin fasinjojin ba. Ofishin Jakadancin Najeriya a Jeddah, karkashin Jakada Muazam Nayaya, ya shiga lamarin tun daga farko tare da tuntubar hukumomin Saudiyya domin kare mutanen.
Bayan tsare su, hukumar NDLEA daga Najeriya ta shiga binciken tare da tabbatar da cewa ba su da hannu cikin lamarin. Sanarwar ta bayyana cewa ofishin jakadancin ya ci gaba da kai ziyara gidan yari, ya bayar da taimakon lauya, sannan ya kasance cikin tuntuba da hukumomin Saudiyya har zuwa lokacin da aka wanke su. An saki Maryam da Bahijah a ranar 14 da 15 ga Satumba 2025, inda suka dawo gida ranar 5 ga Nuwamba.
Abdulkadir ya ce an kuma ɗaga hani na tafiya da aka kakaba wa Abdulhamid Sadieq a ranar 2 ga Disamba 2025, kuma ana kammala shirye-shiryen dawowarsa gida. Ya ce sakin mutanen ya nuna jajircewar Najeriya wajen kare ‘ya’yanta a ƙasashen waje, bisa tsarin 4D na shugaban ƙasa Bola Tinubu.