Yadda aka yi bikin naɗa Rarara sarkin wakar ƙasar Hausa a Daura

[ad_1]



Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruk Umar Faruk, ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasar nan na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa.

An yi bikin naɗin sarautar ne a garin Daura a ranar Asabar 13 ga watan Disamba, 2025 domin karrama rawar da Rarara yake takawa wajen haɓaka waƙoƙin Hausa da kuma tasirin da yake da shi a fagen nishaɗi da al’adu.

Tun da farko mawaƙin da kansa ya wallafa goron gayyatar naɗin sauratar da za a yi masa a shafinsa na Facebook, a ranar 9 ga watan Disamba, 2025.

Rarara ya ce: “Ina gayyatar kowa da kowa zuwa wajen naɗin sarautata, mai taken ‘Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa’ sarautar da mai Alfarma Sarkin Daura ya yi min.

“Za a yi naɗin a fadar Mai Martaba Sarkin Daura a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025, insha’Allah Allah.”

Bikin naɗin sarautar ya samu halartar manyan mutane, mawaƙa, jarumai, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibirin, Ali Nuhu da sauransu, inda masoya da magoya bayan mawaƙin suka nuna farin cikinsu.

Masoyan mawaƙin sun bayyana cewa wannan karramawa ta dace da gudunmawar da Rarara ya bayar ga al’adun Hausawa.

Rarara, wanda ya shahara wajen yin waƙoƙin siyasa da na zamantakewa, ya daɗe ana damawa da shi kuma yana daga cikin manyan mawaƙa a Arewacin Najeriya.

Sabuwar sarautar da aka yi masa na nuni da amincewa da gudunmawarsa wajen bunƙasa waƙa a harshen Hausa da kuma tasirinsa a cikin al’umma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *