Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa
[ad_1]
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa.
Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su.
Mai magana da yawun, su Madam Rose Emmanuel David a lokacin da take zantawa da manema labarai ta ce, an tsare wasu mazajensu ta hanyar aikata ƙananan laifuffuka sama da shekara guda.
Rose ta jaddada cewa hakan ya jefa su cikin halin wahala matuƙa musamman wajen shawo kan matsalolin iyali, saboda hakan ya tilasta musu yin sana’o’in da ba su dace da su ba domin ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da ciyar da ‘ya’yansu.
Sun yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya da hukumomin soji sun shafe shekaru suna yin afuwa ga ’yan Boko Haram, ’yan fashi da sauran masu aikata muggan laifuka.
“Don haka ya zama wajibi su bayyana ra’ayinsu, ta hanyar roƙo a madadin mazajensu da ke tsare a ofishin ’yan sandan Soja (MP) da ke Maiduguri ko su ma sa samu ‘yancinsu da kuma haɗuwa da mu iyalansu.”
“Muna nan a madadin mazajenmu da aka tsare sojojin Nijeriya a ofishin ’yan sandan Soja na runduna ta 7 da ke Maiduguri don miƙa kokenmu.”
“Muna cikin tawali’u da neman jin ƙai da gafara, kasancewar da yawa an tsare su tsawon watanni da shekaru kan laifuka dabam-daban, tun daga lokacin sun amince da kura-kuransu, sun yi tunani sosai, kuma yanzu suna neman dama ta biyu don yi wa ƙasarsu hidima.
“Muna cikin girmamawa muna kira ga mai girma shugaban ƙasa, kuma babban kwamandan sojojin ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya yi musu afuwar shugaban ƙasa.”
“Muna kuma kira ga majalisun dokoki na ƙasa, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da dukkan ’yan Nijeriya da su goyi bayan wannan roƙo na mu don ganin an sako mana mazajenmu, wadda ya kamata a tuna cewa, an yi afuwa ga tubabbun ‘yan tada ƙayar baya da ‘yan bindiga da suka taɓa tayar da fituntuni a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link