Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar

[ad_1]



Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan.

Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an da ke barin gado bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnan Jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya godewa ’yan muƙarrabansa bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

“Gwamnan ya bayyana mahimmancin ’Yancin kan Nijeriya, ya kuma yi kira ga dukkan ’yan Nijeriya da su yi aiki tare da Shugaban Ƙasa domin gina ƙasa mai zaman lafiya da tsaro da wadata da kyakkyawar makoma ga kowa da kowa.

” Gwamnan ya sauke dukkan kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da hukuncin Kotun Ƙoli ya shafa na naɗin nasu nan take.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *