Gobara Ta Ƙone Wani Sashi Na Maƙabarta A Kano
[ad_1]
Gobara ta tashi a Maƙabartar Abbatuwa da ke karamar hukumar Fagge ta jihar Kano a ranar Laraba, 21 ga Janairu, 2026, inda ta ƙone sassa da dama na maƙabartar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce wani mazaunin yankin, Bashir Hassan, ne ya kai rahoton gobarar da misalin karfe 2:02 na rana. “Nan take, jami’anmu daga Hedikwatar Hukumar suka tafi zuwa wurin da lamarin ya faru,” in ji sanarwar.
- “Ba Neman Kuɗi Nake Yi Ba, Na Shiga Siyasa Ne Don Ceto Al’umma” – Tsohon Shugaban DSS
- AFCON 2025: CAF Ta Ci Tarar Algeria, Ta Dakatar Da Ƴan Wasanta
Da isowarsu, “Wani ɓangare na maƙabartar ya riga ya fara ci da wuta wacce ta bazu da hanzari saboda kasancewar busassun ciyayi a cikin wurin.” Hukumar ta ce, ma’aikatanta sun yi aiki da sauri don kashe gobarar da kuma hana ta yaɗuwa.
“Duk da cewa, an yi nasarar shawo kan gobarar, amma ta yi mummunan tasiri a wasu sassan maƙabartar,” in ji sanarwar. Amma an tabbatar da cewa ba a sami asarar rai ba.
Binciken farko ya nuna cewa, ayyukan mutane ne a wurin ya haifar da gobarar. Da wannan, Hukumar Kashe Gobarar ta yi gargaɗi sosai ga jama’a, musamman masu shan taba, da su “daina shan taba ko ɗaukar harshen wuta a fili a cikin maƙabarta da sauran wuraren da akwai busasshiyar ciyawa, domin hana sake afkuwar lamarin a nan gaba.”
[ad_2]
Source link