Real Mallorca ta sallami kocinta Arrasate

[ad_1]

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Mallorca ta sanar da cewa ta raba gari da kocinta, Jagoba Arrasate, sakamakon rashin kataɓus da ƙungiyar ke yi a gasar La Liga.A halin yanzu, Mallorca na matsayi na 18 a teburin La Liga, bayan da ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Celta Vigo a ranar Lahadi.

Wannan ita ce rashin nasara ta uku a jere da ƙungiyar ta yi, kuma ta 13 ke nan a bana haɗi da canjaras shida.

A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce, “Mallorca ta kawo ƙarshen aikin Jagoba Arrasate a matsayin kocin ƙungiyar.”

Ta ƙara da cewa matakin da ta ɗauka na da nasaba ne da ƙoƙarin ƙungiyar na sauya halin da ake ciki tare da fuskantar ragowar kakar wasa cikin tsari mafi kyau.

Arrasate shi ne ya jagoranci Mallorca ta kammala kakar bara a tsakiyar tebur a kakarsa ta farko, sai dai a kakar bana ya samu nasara ne a wasanni shida kacal daga cikin 25 na gasar lig.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *