Mutum 1 Ya Rasu Yayin Da Sojoji Suka Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Ƙauyukan Benue
Aƙalla mutum ɗaya ne ya rasa ransa bayan ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Olojo, Ojantelle da Edikwu Icho a Jihar Benue.
Harın ya faru da misalin ƙarfe 1:45 na rana a ƙaramar hukumar Apa, inda maharan suka riƙa harbe-harbe wanda ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 7
- Shugaba Tinubu Ya Haɗa Taron Shan Ruwa, Ya Bukaci Haɗin Kai Daga Gwamnoni
Sojoji da wasu jami’an tsaro sun isa cikin gaggawa, tare da fafatawa da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
A yayin harin, wani mazaunin Edikwu Icho mai suna Ngbede Okpe Agabaidu ya mutu bayan an harbe shi.
Daga bisani aka kai gawarsa ɗakin ajiye gawarwaki na yankin.
A yanzu haka rundunar soji ta fara sa ido ta sama tare da ci gaba da sintiri domin gano da kuma kama maharan da suka tsere.