El-Rufa’i ya maka ICPC a Kotu
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El‑Rufai, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana ƙalubalantar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, ICPC, kan tsare shi da kuma binciken da ta yi a gidansa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa El-Rufai ya roƙi kotun ta ayyana takardar izinin binciken gidansa a matsayin mara inganci, tare da bayyana cewa an tauye masa haƙƙoƙinsa da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
A ƙunshin ƙarar, El-Rufai ya kuma buƙaci Kotun ta umurci ICPC da ta mayar masa da dukkan kayayyakin da aka kwaso daga gidansa, sannan ta hana hukumar amfani da su a matsayin hujja a gaba.
Ana iya tuna cewa, a ranar 16 ga watan Fabarairu ne El-Rufai ya kai kansa ofishin EFCC domin amsa gayyatar da hukumar yi masa, amma aka tsare shi.
Daga bisani, a daren 18 ga Fabrairu, aka miƙa shi hannun ICPC, wadda ita ma ke gudanar da nata binciken daban.
Adekeye ya ce duk da cewa ya shafe kwanaki takwas ana tsare da tsohon gwamnan, har yanzu ICPC ba ta ba shi beli ba, duk da cewa lauyoyinsa sun shigar da buƙatar beli tun ranar 19 ga Fabrairu.
Ya ƙara da cewa, ba a nuna musu wata sahihiyar takardar kotu da ke ba da izinin ci gaba da tsare shi ba, duk da wuce sa’o’i 48 da doka ta tanada.
Ya bayyana cewa jami’an ICPC sun binciki gidan El-Rufai da ke Aso Drive a Abuja ranar 19 ga Fabrairu, lamarin da lauyansa, Ubong Akpan, ba ya bisa ƙa’idar da doka ta tanada, yana mai cewa an yi binciken ne da takardar izini mara inganci.
A sakamakon haka, El-Rufai ya nemi kotu ta yi watsi da takardar izinin binciken, yana mai cewa ba ta cika ka’idojin doka ba, kuma ta hana amfani da kayayyakin da aka ƙwace a duk wata shari’a da za a shigar a kansa.
Rahotanni sun kuma nuna cewa akwai shari’o’i biyu da suka shafi El-Rufai da za su zo gaban kotu a wannan mako, ciki har da ƙarar kare haƙƙoƙin ɗan-Adam da aka shigar kan Gwamnatin Tarayya, ICPC, EFCC da DSS, wadda za a saurara ranar 25 ga Fabrairu a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Lauyoyinsa sun ce halin da ake ciki, El-Rufa’i ya zarce wa’adin ci gaba da tsare shi wanda doka ta tanada, inda suka koka da cewa har yanzu ana hana iyalansa da lauyoyinsa samun damar ganinsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link