Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara
[ad_1]
Babban kwamandan runduna ta 2 na Sojojin Nijeriya kuma Kwamandan Sashi na 3 na atisayen Fansar Yamma, Manjo Janar Chinedu Nnebeife, ya jagoranci wani sumame da ya kai ga ceto mutanen da aka sace a jihar Kwara a ranar 9 ga Oktoba, 2025.
Manjo Janar Nnebeife ya gudanar da wannan aikin ne yayin ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Idofin, Oba Pius Oluwole, bayan harin ƴan bindiga a ƙauyen Olegbede, kimanin kilomita 12 daga Idofin Ayekale, inda mutane uku suka rasa rayukansu.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na runduna ta 2, Watchan Polycarp Okeya fitar, an bayyana cewa GOC ya kai ziyarar ne don duba yankin da harin ya auku, kusa da dajin Babasango a ƙaramar hukumar Omu-Aran.
Okoye ya ce Oba Oluwole ya danganta harin da matsalar tsaron yankin dajin Babasango. A nasa ɓangaren, Janar Nnebeife ya jajanta wa Sarkin tare da tabbatar masa cewa dakarun Soji za su ci gaba da kai hare-hare don kawar da ƴan bindiga da sauran masu laifi daga dajin.
A yayin ziyarar aiki zuwa sansanin sintiri na Babanla, GOC tare da Sojojinsa sun shiga dajin Babasango, inda suka ceto mutum biyu da aka sace, sannan suka mika su ga Sarkin Idofin, Oba Oluwole.
[ad_2]
Source link