Kisan Gilla: An tura dakarun soji zuwa dazukan Kwara — Shettima

[ad_1]



Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da tura rundunar sojin Najeriya zuwa dazukan Jihar Kwara, bayan harin da ya auku a yankin Woro da ne Ƙaramar Hukumar Kaiama, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 100.

Shettima, ya ce an tura sojojin ne domin daƙile hare-hare da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Ya bayyana kisan gillar ya girgiza ƙasa tare da saɓa wa hakkin ’yan ƙasa na rayuwa da gudanar da addininsu cikin kwanciyar hankali.

Mataimakin ya faɗi hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai Ilorin, inda Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya tarbe shi.

Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa Gwamnatin Tarayya na aiki tare da gwamnatin jihar domin inganta tsaro da kuma tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

Shettima ya kuma isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga al’ummar Kwara, tare da umarnin da aka bai wa hukumar NEMA domin taimaka wa iyalan waɗanda harin ya shafa.

Gwamna AbdulRazaq, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan gaggawar tura sojoji da jami’an tsaro, inda ya ce tuni dakarun tsaro suka fara aiki don hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.

Hakazalika, sarakunan gargajiya da shugabannin yankin sun yi godiya kan matakin da gwamnati ta ɗauka, tare da kira da a ci gaba da samar da tsaro a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *