HOTUNA: Wike Ya Buɗe Gidan Rediyo Don Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Ribas
[ad_1]
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya buɗe wani sabon gidan rediyo mai suna Majority FM 89.5 domin taimakawa sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a Jihar Ribas a shekarar 2027.
An kafa gidan rediyon ne a cikin ofishin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors da ke Fatakwal.
- Babban Sakataren AL Ahmed Aboul Gheit: An Sada Zumunta Mai Zurfi Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa
- Rigakafin Cutar Shanyewar Barin Jiki
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna Wike yana zagayawa a cikin gidan rediyon tare da duba kayayyakin aiki da kuma tattaunawa da ma’aikata yayin ƙaddamar da shi.
Wike ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen yaɗa saƙonnin yaƙin neman zaɓen Tinubu a faɗin Jihar Ribas gabanin zaɓen 2027.
Masu sharhi kan siyasa sun ce wannan mataki na ƙara nuna ƙarfin tasirin Wike a siyasar jihar.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Wike da ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan yadda gidan rediyon zai gudanar da ayyukansa ba.
Ga hotunan:





[ad_2]
Source link