CMG Ya Yi Taron Manema Labarai Kan Bikin Bazara Na Shekarar 2026

[ad_1]

Yau Laraba 4 ga wannan wata, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice ya yi taron manema labarai kan bikin bazara na sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin ta 2026 a nan birnin Beijing, inda aka yi bayani kan shirye-shiryen da za a gabatar da sabbin fasahohin da za a yi amfani da su yayin bikin. Kana an gabatar da sunayen masu jagorantar bikin, da fasalin fasaha na dandalolin bikin.

A ranar 16 ga watan Fabrairun dake tafe da yamma, da misalin karfe 8, za a gabatar da bikin bazara na shekarar doki ta gargajiyar kasar Sin kai tsaye a gidan talibijin na CCTV da sauran wasu dandalolin yanar gizo.

Abun lura shi ne, gidan talibijin na kasa da kasa na kasar Sin ko CGTN a takaice zai gabatar da bikin kai tsaye cikin harsuna 85 da suke hada da Turanci da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci cikin hadin gwiwa da kafofin watsa labarai sama da 3300 dake kasashe da yankuna fiye da 200 a fadin duniya. (Mai fassara: Jamila)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *