Kasuwar Musayar ‘Yan Kwallo: Kante Ya Kammala Komawa Fenerbahce
Kungiyar kwallon kafa ta Fenerbahce dake buga gasar Turkish League n kasar Turkiyya, ta kammala daukar dan wasan tsakiyar kasar Faransa N’Golo Kante daga kungiyar Al-Ittihad ta kasar Saudia, tunda farko dai burin Kante na komawa Turkiyya ya so ya sha ruwa bayan yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu ta fasu.
Amma daga bisani al’amura sun daidaita tsakanin kungiyoyin biyu inda aka kammala cinikin cikin sauki, Kante ya shiga rudani a lokacin da Fenerbahce ta fitar da wata sanarwa inda take zargin Al-Ittihad da rugujewar wannan ciniki.
Fenerbahce ta yi ikirarin cewa Al-Ittihad ta kasa gabatar da takardun da suka wajaba domin kammala cinikin, yarjejeniyar dai ta kunshi musaya da dan wasan Morocco Youssef En-Nesyri wanda zai koma Al-Ittihad, amma kuma Fenerbahce ta tabbatar a ranar Laraba cewa an warware matsalar kuma tsohon dan wasan Chelsea Kante, ya koma kungiyar bayan shekaru biyu da rabi a Saudi Arabia.
Kante, mai shekaru 34, ya koma Al-Ittihad daga Chelsea a shekarar 2023, bayan ya lashe gasar zakarun Turai, gasar Premier, gasar Europa League da kuma gasar FA tare da kungiyar ta London, ya koma Chelsea daga Leicester City a shekarar 2016, bayan ya jagoranci Foxes din wajen lashe gasar Premier.