Sojoji sun ceto mutum 11 da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja
[ad_1]
Sojoji sun ceto wasu mutum 11 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon kwana 92 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun kubutar da mutanen ne bayan da suka gano shirin ’yan bindigar na sauya wa mutanen wuri a cikin duhun dare, a yankin Gidan Duna-Amale.
A sanarwar ta fitar ta shafinta na X, rundunar ta ce bayan kyamarorinta na hangen nesa a cikin duna dun gano motsin ’yan bindigar da mutanen, sojoji suka bi su, suka tare su, amma bata-garin suka tsere zuwa cikin daji suka bar mutanen.
Mutanen da aka ceto a cewar sanarwar sun hada da maza manya biyar da mata uku da kananan yara uku, wadanda tun ranar 26 ga watan Oktobar 2025 aka sace su daga yankin Gadar Mallam Mamman da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Rundunar ta bayyana cewa wannan nasarar ta jaddada tasairin amafni da kayan fasahar zamani a ayyukanta na tsabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummomin Najeriya, a ko’ina, ba dare ba rana.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link