Amurka Za Ta Ƙara Bai Wa Nijeriya Kayan Aikin Soji Don Yaƙar Ta’addanci
[ad_1]
Gwamnatin Amurka ta ce za ta ƙara wa Nijeriya tallafin kayan aikin soji na zamani domin taimaka mata wajen yaƙar ‘yan ta’adda, musamman masu alaƙa da ƙungiyar ISIS.
Wani babban jami’in sojin Amurka mai kula da Afirka, Laftanar Janar John Brennan, ya ce ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) na ƙara haɗa kai da sojojin ƙasashen Afirka, ciki har da Nijeriya, domin fuskantar barazanar tsaro a yankin Sahel.
- Mataimakin Gwamna Yusuf Bai Halarci Taron Sauya Sheƙar Maigidansa Zuwa APC Ba
- Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Fashi da Makami A Abuja, Sun Kama Wani Mutum
Ya bayyana cewa Amurka na fuskantar matsin lamba kan yadda za ta taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro a ƙasashe irin su Nijeriya da Somaliya, waɗanda ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.
Brennan ya ƙara da cewa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya na da muhimmanci, musamman bayan rahotannin kai hare-hare da ake danganta wa ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi a Nijeriya.
Matakin na Amurka na zuwa ne domin ƙarfafa sojojin Nijeriya wajen kare ƙasar da kuma rage barazanar ta’addanci.
[ad_2]
Source link