Mutane 62 da aka sace sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Katsina




Mutum 62 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sama da wata guda sun tsere bayan rundunar soji ta kai farmakin sama da ƙasa a maboyar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar ƊanMusa, Jihar Katsina.

Farmakin da aka kai a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:10 na yamma ya gudana ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri, inda dakarun sojin sama da na ƙasa suka haɗa kai wajen kai hari a kauyen Jigawa Sawai, wanda ke iyaka da Jihar Zamfara.

A cewar sanarwar da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Katsina ta fitar, farmakin ya tilasta ’yan bindigar guduwa, lamarin da ya ba wa mutanen da aka yi garkuwa da su damar tserewa cikin ruɗani.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsere sun bayyana cewa sun rabu da juna yayin tserewa, amma an tattaro su daga sassa daban-daban.

Gwamnatin jihar ta ce mafi yawan waɗanda aka ceto an sace su ’yan asalin ƙauyen Sayaya a Ƙaramar Hukumar Matazu, a wani farmaki da aka kai da daddare ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, daga wani gungun ’yan bindiga da ake kira na Muhammadu Fulani.

A halin yanzu, mutum 12 daga cikin waɗanda suka tsere suna samun kulawar likita a Asibitin Matazu, yayin da 16 ke a sansanin soji na Kaiga Malamai. Ana ci gaba da tantance lafiyar sauran kafin a haɗa su da iyalansu.

Kwamishinan Tsaro, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa an tura Sojin Sama zuwa ƙananan hukumomin Matazu da Bakori domin dakile hare-haren ’yan bindiga da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Gwamna Dikko Radda ya yaba da ƙwazon jami’an tsaro, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa na da niyyar kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

Ya kuma tabbatar wa iyalan waɗanda aka ceto cewa za a haɗa su da ’yan uwansu bayan an kammala duk wasu bincike da jinyar da ake yi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *