Salah Zai Bar Liverpool Bayan Shafe Shekaru 9 A Ƙungiyar
[ad_1]
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Masar, Mohamed Salah, ya sanar da cewa zai bar Liverpool a ƙarshen kakar wasa ta bana, bayan ya shafe shekaru tara a ƙungiyar.
Salah mai shekaru 33 ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan jita-jitar da aka daɗe ana yi game da makomarsa.
- Kusan Shugabannin Kamfanoni 100 Ne Suka Taru Domin Halartar Dandalin Bunkasa Kasar Sin
- Atiku Ya Nuna Damuwarsa Kan Kama ‘Yan Adawa, Ya Nemi A Saki El-Rufai
Ya ce lokaci ya yi da zai sauya sheƙa.
Ya koma Liverpool daga AS Roma a shekarar 2017, kuma ya zama ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan ƙungiyar.
Ya zura ƙwallaye 255 a wasanni 435, wanda ya sa ya zama na uku a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a tarihin kulob ɗin.
Ya taimaka wa ƙungiyar ta lashe manyan kofuna, ciki har da Premier League, UEFA Champions League, da FA Cup.
Haka kuma ya lashe kyaututtuka da dama, ciki har da Golden Boot sau huɗu.
Da yake magana kan zamansa a kulob ɗin, Salah ya ce Liverpool ta zama wani muhimmin ɓangare na rayuwarsa, tare da gode wa abokan wasansa da magoya baya.
“Barin kulob ba abu ne mai sauƙi ba,” in ji shi.
“Kun ba ni mafi kyawun lokaci a rayuwata. Wannan kulob zai ci gaba da zama gida a gare ni.”
Liverpool ta kuma tabbatar da cewa Salah zai bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare.
Kulob ɗin ya ce ya sanar da wannan tun da wuri ne domin girmama magoya baya.
Duk da haka, Salah ya ce ya mai da hankali wajen taimaka wa ƙungiyar ta kammala kakar wasa yadda ya kamata.
[ad_2]
Source link