Harin Amurka ya ragargaza Lakurawa — Rundunar Sojin Najeriya
[ad_1]
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da samun gagarumar nasara bayan harin da Amurka ta jagoranta a maboyar ’yan ta’addan Lakurawa a Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.
Mukaddashin Daraktan Watsa Labarai na rundunar, Kanar Appolonia Anele, ta bayyana a ranar Litinin cewa dakarun Combat Intelligence Battalion VII, bisa sahihin bayanan sirri kan motsin ’yan ta’adda a yankin Kaurau, sun haɗa kai da rundunar US AFRICOM wajen kai farmaki kan sansanonin da ke cikin dajin Bauni, kusa da kauyukan Waria da Alkassim, a ranar 25 ga Disamba.
Anele ta ƙara da cewa binciken da aka yi a ranar 26 ga Disamba ya tabbatar da tarwatsa sansanonin ’yan ta’addan, lamarin da ya raunana ƙarfinsu sosai.
A wani samame dabam, sojojin 1 Brigade, Combat Team 12 da ke sansanin Jabo a Jihar Kebbi, sun gano tarkacen da ake zargin na jirage marasa matuki ne da kuma sassan makamai a Kajiji, Karamar Hukuamr Tambuwal.
Rahoton farko daga injiniyoyin rundunar (EME) ya nuna cewa wasu daga cikin tarkacen na makami mai linzami na Tomahawk ne.
Rundunar sojin ta tabbatar wa jama’a cewa bincike yana ci gaba domin tattara sauran sassan makaman cikin tsaro, tare da kira ga al’umma da su rika sanar da hukumomi idan suka ga wani abu da ake zargi.
Sojojin sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a Arewacin Najeriya.
(IN)
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link