Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Shekara-shekara Na Dandalin Tattaunawa Kan Ci Gaban Kasar Sin Na 2026
[ad_1]
A yau Lahadi 22 ga wannan wata, firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan batun ci gaban kasar Sin na shekarar 2026 tare da gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15 shi ne taswirar samun ci gaban kasar Sin, kana shi ne sabuwar damar samun ci gaban duniya baki daya.
Li Qiang ya bayyana cewa, ya kamata mu bi tunanin bude kofa ga kasashen waje da yin kokari, wato fadada yin ciniki cikin ‘yanci tare da sa-kaimi ga yin kirkire-kirkire. Sha’anin shige da fice na kasar Sin shi ne ciniki mai adalci bisa tsarin ka’idoji, kasar Sin za ta ci gaba da sa-kaimi ga bude kofa ga kasashen waje, da shigar da karin kayayyakin kasashen waje masu inganci zuwa kasar Sin, da yin kokari tare da bangarori daban daban wajen kyautata ciniki mai adalci don raya cinikin duniya baki daya.
Li Qiang ya kara da cewa, Sin ta samu fifiko kan wasu sana’o’i ta hanyar yin kwaskwarima mai zurfi da yin kirkire-kirkire, ba ta dogaro da rancen kudi ko manufar ba da kariya a kansu ba, kuma kokarin jama’a da kamfanonin Sin ya fi muhimmanci a wannan fanni. Kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da odar kasuwanci mai adalci, tare da fatan bangarori daban daban za su kara yin mu’amala da hadin gwiwa da juna don sa- kaimi ga tabbatar da tsarin samar da kayayyaki da sayar da su yadda ya kamata. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link