Dalilin da ya sa na fara karatun digirin farko a fannin shari’a a jami’a – Sarki Sanusi
[ad_1]
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce shawarar da ya yanke ta fara karatun digirin farko a Jami’ar Northwest da ke Kano wani yunkuri ne na cika burin rayuwarsa na karantar fannin shari’a.
Sarkin ya kuma bayyana karatun shari’a a matsayin ginshikin gina al’umma mai zaman lafiya da adalci.
Ya bayyana hakan ne jim kadan da kamala daukar darasi a jami’ar ranar Alhamis, inda ya ce duk da cewa yana da digirin digirgir, ya dade yana sha’awar karatun shari’a.
Ya kara da cewa wannan shi ne digiri a fanni na uku da yake nema, bayan ya yi karatun tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sannan daga baya ya yi wasu karatuttukan daban-daban.
“Na kan ce aji shi ne matsugunina na asali. Nakan yi farin ciki idan ina karatu ko koyarwa. Wannan dama ce ta yin karatun da na dade ina sha’awa. Doka tana ko’ina, taimakawa wajen gudanar da iyali, bayar da kwangila, kula da dukiya, rabon gado, har ma yadda ake tuƙi a kan hanya. Ita ce kariya ga al’umma mai mutunci da kwanciyar hankali.
“Yana da amfani a fahimci doka, amma abu mafi muhimmanci, ita ce ginshikin da ke rike al’umma. Ranar da babu doka da oda, mai ƙarfi zai yi abin da ya ga dama, mai rauni kuma zai sha wahala,” in ji shi.
Game da dalilin da ya sa ya zabi Jami’ar ta Northwest, Sarkin ya ce ita ce ta ba shi gurbin karatu kuma mallakar jiharsa ce, wanda ya ce ya zama wajibi ya tallafa mata.
“Muna raina malamanmu na cikin gida, amma matakin iliminsu iri daya ne da na waje. Idan za ka yi karatun shari’s, ka yi shi a Najeriya. Me ya sa za ka je ka yi karatun dokar Birtaniya alhali ba a can za ka zauna ba?” in ji shi.
‘Dalibi da safe, sarki da yamma’
Da yake bayani kan yadda zai daidaita aikinsa na sarauta da karatun jami’a a lokaci daya, Sarkin ya ce: “Dalibi nake da safe, sarki kuma da yamma. Talata, Laraba da Alhamis nake zuwa aji, yayin da Litinin da Juma’a nake zaman fada a lokutan da aka saba.
“Idan ba zan iya zuwa lakcar ba, zan shiga ta intanet na saurara. Jami’ar ta sassauta min wajen daidaita jadawalin karatuna,” in ji shi.
Da yake kwatanta rayuwar makaranta ta yanzu da kuma ta baya, Sanusi ya ce ladabi da jajircewar daliban sun birge shi sosai.
“A shekarun 1970, a kan kujerun katako nake zama. Yau kujerun kuma sun fi kyau, kuma na ga matasa maza da mata masu son yin karatu. Shari’a tun da dadewa fanni ne mai tsari, kuma na ji daɗin zama tare da su,” in ji shi.
Sarkin ya yi kira ga matasa da manya su rungumi koyon ilimi a kowane lokaci. “Babu wanda ya yi ƙanƙanta ko ya yi girma da zai ce ba zai je makaranta ba. Yawan ilimi yana inganta mutum a matsayin ɗan ƙasa. Kwanana uku kacal a nan amma na koyi abubuwa da dama. Dole mu nemi ilimi domin shi ne ke inganta mu a matsayin mutane da ’yan ƙasa,” in ji shi.
Sanusi ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su zuba jari sosai a fannin ilimi, musamman a bangaren kayan aiki kamar fasahar sadarwa, wutar lantarki mai dorewa da kuma walwalar ma’aikata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link