Ko Kin San… Dalilan Kamuwa Da Karin Mahaifa (Fibroid) (1)

[ad_1]

Fibroid ba sabon abu bane a bakinmu domin na tabbata kun dade kuna ji ana fadar sa, sai dai watakila ba ku san cewa yana iya kawo matsaloli da dama ga matan ba ciki kadai ba har da matsala ta rashin haihuwa.

Bari mu kalli dalilan da ke kawo FIBROID har su girma, da abin da za a iya yi don kare kai daga kamuwa da shi.

1-Hormones – ESTROGEN YANA BA DA PRAGESTERONE

Wato wani sinadari ne da jiki ke samarwa domin sarrafa ayyuka daban-daban na jikin kamar girma da sauransu. Wadannan abubuwa suna taimakawa wajen inganta lafiyar mahaifa, amma idan suka yi yawa, suna iya kawo ciwon fibroid har ya girma sosai.

Estrogen, ana samun sa ne sosai a jikin mace a tsakanin shekarun haihuwa (shekaru 16 zuwa 50). Don haka ki kula da hormones dinki ta hanyar cin abinci mai kyau, rage damuwa, da motsa jiki.

2. Gado: Idan Uwa, ’yar’uwarki, ko ’yar gidanku ta taBa yin fibroid, to ke ma kina da yuwuwar samunsa.

3. Fara juni al’ad da wuri. Fara jinin al’ada da wuri (kafin shekaru 12) yana kara hadarin samun ciwon fibroid. 4. Shekaru (30–50): Lokacin da mace ta kai shekaru 30 zuwa 50, a samun canje canjen hormones sosai.

Ki kula da jikinki sosai a wannan lokaci, ki ci abinci mai kyau, ki motsa jiki, ki rika duba lafiyarki akai-akai. 5. Kiba: Kiba na kara yawan estrogen a jiki, wanda ke taimaka wa fibroid su girma sosai. Ki kula da nauyinki, ki rage cin abinci mai sa taruwar kitse da sukari, ki motsa jiki kullum.

6. Abinci: Cin Jan nama, madara mai sa taruwar kitse, da gishiri da yawa suna kara hadarin fibroid. Ki ci kayan lambu, kayan itace, da abinci mai dauke da ganyayyaki domin rage hadarin samun Fibroid.

7. Giya: Shan giya yana kara yawan Estrogen hormones a jiki, wanda ke taimaka wa fibroid su girma. Ki guji giya gaba daya domin lafiyarki da kuma domin ki kare mahaifar ki daga FIBROID.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *