Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Japan Ta Aiwatar Da Matakan Kariya Na Bai-daya Don Tsoma Baki A Batun Taiwan
[ad_1]
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya jaddada cewa, idan Japan, ta kowace irin hujja, ta dauki “matakan kariya na bai-daya” don tsoma baki a cikin batun Taiwan, hakan zai zama wani nau’i na hari a kan kasar Sin, kuma kasar Sin za ta mayar da martani mai tsanani.
Fu Cong ya fadi haka ne a jawabin da ya gabatar a muhawara ta taron kwamitin musamman dake kula da kundin tsarin MDD da karfafa rawar da MDD ke takawa na shekarar 2026, wanda aka gudanar a jiya Laraba.
Fu Cong ya kara da cewa, kwanan nan, firaministar kasar Japan ta bijire wa tarihi, inda ta fito fili ta danganta Taiwan ta kasar Sin da “yanayin dorewa” na Japan, har ma ta yi tunanin banza na mayar da martani bisa ga kawancen Japan da Amurka, da nufin tsoma baki cikin batun Taiwan da karfin soja bisa hujjar “matakan kariya na bai-daya”.
Fu Cong ya nuna cewa, Katobarar firaministar Japan ta saba wa muhimman ka’idojin da ke cikin kundin tsarin MDD game da mutunta mulkin kai da cikakkun yankunan kasa, da ma rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe, wadda kuma kalubale ne ga tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na II, kuma ya kamata kasashe masu son zaman lafiya su zama a ankare tare da nuna adawa da hakan. (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link