Mutane Da Dama Sun Mutu, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Sokoto
[ad_1]
Mutane da dama sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata bayan wani harin da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa al’ummar Dabagin Yari a karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.
Harin, wanda ya faru a daren Laraba, ya kuma haifar da sace dimbin mazauna yankin, ciki har da mata da yara, a cewar majiyoyin yankin.
- Darussa Daga Ramadan Na (1)
- Mark Zuckerberg Zai Gurfana A Gaban Kotu A Amurka
Mai sharhi kan tsaro, Bakatsine ya bayyana cikakkun bayanai game da lamarin a cikin wani rubutu da ya yi a shafin sada zumunta na X a ranar Alhamis, yana mai bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin tausayi.
Harin ya jefa al’ummar cikin damuwa, inda iyalai ke jimamin rashin ‘yan uwansu da aka kashe da waɗanda aka tafi da su.
Har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoton, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba wadda ke tabbatar da adadin waɗanda suka mutu da kuma adadin waɗanda aka sace.
Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ‘yansandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufa’i, ya ce, zai fitar da rahoto bayan ya tabbatar da rahoton.
Duk da haka, har yanzu bai bayar da karin bayani ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.
[ad_2]
Source link