Duk da ragin kuɗin mai, har yanzu direbobi ba su rage kuɗin mota ba
[ad_1]
Binciken Aminiya ya gano cewa har yanzu direbobin motocin haya ba su rage kuɗin mota ba duk da sauƙin farashin mai da ake samu a Najeriya.
A halin yanzu gidajen mai na sayar da litar fetur a kan N739 zuwa 850 saɓanin a baya da yake kamawa tsakanin 910 zuwa 960, tun bayan cire tallafin da Gwamnatin Tinubu ta yi a shekarar 2023.
A zantawar da Aminiya ta yi da wasu direbobi, sun bayyana cewa tabbas farashin mai ya sauƙa amma farashin sauran kayayyakin gyara na nan yadda yake.
Sun ƙara da cewa za su rage kuɗin mota idan farashin sauran kayayyakin gyara ya sauka.
Wasu direbobi kuma sun tabbatar da sauƙin farashin man, amma dai sun ce har yanzu ba su rage kuɗin motar ba, saboda da ma can haƙuri suke da ɗan abin da aka samu na riba, wani lokacin ma har asara ake samu a wannan farashin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link