Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kasafin Kuɗi Naira Tiriliyan 1.47 Na 2026

[ad_1]

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kasafin kuɗi na shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.47, bayan ƙara Naira biliyan 109.7 kan abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar tun farko. An amince da daftarin kasafin ne a zaman majalisa da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya jagoranta a ranar Litinin.

Kasafin, wanda ya kai jimillar N1,477,829,666,131ya samu amincewa ne bayan duba shi a Kwamitin Gaba ɗaya da kuma karantawa karo na uku da Magatakardar Majalisar, Bashir Diso, ya yi. Tun da farko, Gwamna Yusuf ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 1.36 mai taken “Kasafin Bunƙasa Ababen More Rayuwa, Ci Gaban Bai-ɗaya da Ɗorewar Tattalin Arziƙi.”

  • Masana Sun Bayyana Yadda Kasafin Kudin 2026 Zai Shafi Tsaro Da Ilimi Da Kiwon Lafiya
  • Hisbah Ta Kama Mutane 9 Kan Yawon Dare A Kano

Da yake yi wa manema labarai bayani, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Husseini Lawan, ya ce ƙarin da aka yi ya samo asali ne daga hasashen ƙarin kuɗaɗen shiga, musamman daga rabon tarayya da kuma harajin VAT. Ya ce an ware Naira tiriliyan 1.048 domin ayyukan raya ƙasa, wato kashi 75, yayin da aka ware Naira biliyan 429 domin kuɗaɗen gudanarwa, wato kashi 25.

Lawan ya bayyana cewa ɓangarorin ilimi da lafiya ne suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin, inda ilimi ya samu kusan kashi 30, sama da ƙa’idar UNESCO, yayin da lafiya ta samu kashi 16, sama da ƙa’idar Abuja Declaration. Ya ƙara da cewa Majalisar ta kuma yi zaman ban-kwana na girmamawa ga marigayi ’yan majalisa biyu, Aminu Sa’ad da Sarki Aliyu Danaji, inda Kakakin Majalisar ya bayyana rasuwarsu a matsayin babban rashi ga jihar Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *