Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala
[ad_1]
A ranar Lahadin da ta gabata ne 2/11//2025, aka wayi gari da rasuwar Alhaji Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala me sittin goma a cikin shirin Dadin Kowa, na tashar Arewa24. An haifi Alhaji Mato Yakubu a garin Dambuwa Rijiya, karamar hukumar Potiskum, Jihar Yobe a 15/8/1967.
Alhaji Mato Yakubu, jarumi ne da yake taka rawa a cikin shiri me dogon zango na Arewa24 wato shirin Dadin Kowa. Baya ga haka jarumin ya shafe tsahon shekaru yana bayar da gudunmawarsa a wasannin dabe tun kafin zuwan Kannywood. Haka kuma ya yi finafinai da dama a cikin masana’antar Kannywood. Malam Nata’ala ya rasu ya bar yara goma, mata hudu, maza shida, da matansa uku. Ya rasu sakamakon ciwon kansa da yake damunsa, bayan doguwar jinyar da ya sha.
Dalilin hakan ya sa shafin RUMBUN NISHADI, jin ta bakin wasu daga cikin abokan sana’arsa na fim, domin jin yadda suka ji rasuwarsa, da kuma irin kyawawan halayan da yake da shi wanda jama’a ba su sani ba, tare da jin irin abubuwan da idan suka ji ko suka gani suke tunawa da shi.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka; Sunana Zahra’u Sale Fantami, wacce aka fi sani da Adaman Kamaye/Adaman Nata’ala:
Inna lillahi wa inna iliahirraji’un, Allah mun gode maka saboda Allah shi ne abun godiya. Mun yi babban rashi na abokin aikin mu wato, Malam Nata’ala Mato Yakubu wanda aka fi sani da Mato Mato, ko ace na Kunduba. Gaskiya mun yi asara babba, musamman yadda muke taka rawa ni da shi a Dadin Kowa, kowa yana son wannan shiri namu to, yau ubangiji ya karbi rayuwarsa. Muna barar addu’ar musulmin duniya bakidaya da su taimaka su yi mana addu’a. Abokiyar zamana Azumi wacce muke barkwanci da shi ba wanda ya taba samun matsala da shi, mutumin kirki ne muna mu’amala daga nan har gida cikin iyalinsa muna komai tare da shi. Duk abin da ya taso a Yobe zai kira mu a yi damu, kai! Allahu akubar Allah ka gafartawa Malam, Allah ka kyauta namu karshen. Al’ummar musulmin duniya muna barar addu’o’inku, dan Allah duk wanda ya san ba zai fadi alkhairi akan dan fim ba to, ya yi shuru. Allah ya yi masa rahma, mu kuma ubangiji Allah ya bamu guruzin tarar da su, Allah ya sa mu ma in mun tashi mu yi kyan karshe, mu cika da kyau da imani. Ni ce Zahra’u Sale Fantami wato Adamanliyan Nata’aliya. Wassalamu Alaikum
Sunana Abdulhurid Ado (Danba’ayino):
Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin rigar yake fado min tun da ya fara jinya har zuwa yanzun nan da kuma sauran abun alkairai da yayi mana muna tare. Mun yi rashi matuka da gaske, Allah yayi masa rahama, Allah ya kula da bayan sa.
Sunana Sarah Aloysius (Edecutibe Producer, Dadin Kowa):
Gaskiya Mun yi babban rashi, ba Dadin kowa kadai ba, Kannywood bakidaya. Malam Nata’ala yana daya daga cikin jigajigan jaruman da masana’antar kannywood ta dogara dasu da fuskar rike aikinsu da muhimmanci. Yana da hakuri da juriya wajen aiki, yana da girmama mutane komai girma ko kankantar mutum, yana da kyauta, abun hannunsa baya rufe masa ido. Malam Nata’ala yana da rike alkawari sosai, ga kyakkawar mu’amala da mutane da kuma barkwanci. Akwai wani lokaci da muka samu matsalar ‘schedule’ na aikin shirin Dadin Kowa, muka kira shi cikin dare cewa, za mu yi aiki da shi washegari, a lokacin bai ma fada mana baya kasar ba, amma haka muka tarar da shi washegari a ‘location’. Haka kuma a lokuta da dama, sai ka ganshi ya zo ‘location’ da kayan tsaraba ya rabawa ‘crew members’. Kawai sai dai muce Allah yayi masa rahma, ya haskaka kabarinsa.
Sunana Fati Al’amin wacce aka fi sani da Maman Badaru:
Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un, wallahi na girgiza da jin rasuwar Malam Nata’ala sosai. Hakika mun yi babban rashin mutumin kirki wanda abin duniya bai rufe masa ido ba. A duk lokacin da muka fita wajan wani aiki ko wata gaiyata da aka yi mana wallahi shi ne yake shugabantar tafiyar. Amma abin da zai baki sha’awa da rayuwarsa duk wani alkhairi da aka samo to, fa baya bari a wajansa. Ni yake bawa ya ce, na ajjiye har sai mungama samun abin da aka bamu, sannan ya ce Fati na yarda da amanarki ki raba ki bawa kowa hakkinsa (Kuka). Ni kuma sai na raba na bawa kowa, sannan na fitar masa da na sa dan shi ne ya kawo harkar. Wani lokacin har nakan yi bakin jini a wajan wasu su ce na cika masa, ni kuma sai na ce da bai kawo aikin ba fa?. Allah ya ji kansa da rahma ya sa aljanna makomar sa. Wallahi ina tuna shi ta son kawo wa al’umma alkhairi, ba tare da bakin ciki ba, ga son ciyarwa ga al’umma, Allah yayi masa rahma.
Sunana Alh. Dauda Adakawa, wanda aka fi sani da Malam Barau na Dadin Kowa:
Rasuwar malam Nata’ala ta girgiza ni da kyau, kasancewar ni ne kamar sa’ansa kuma aboki wanda ko harkar rashin lafiyarsa, da ni muke yawan magana da yan’uwansa, musamman Sadi Potiskum. Malam yana da karamci, jin kai, da son abokan aikin sa, sannan mai son kowa ya samu alkhairi ne. Gaskiya akwai abubuwan da za mu kare rayuwar mu muna tuna Malam Nata’ala da shi, kamar; Kyauta, gaskiya, da son jama’a.
[ad_2]
Source link