Wang Yi: Ba Wata Kasa Dake Da Ikon Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidan Sauran Kasashe Bisa Radin Kan Ta
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna da takwaransa, kana mataimakin firaministan kasar Pakistan Ishaq Dar kan manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu karo na 7 a birnin Beijing.
Yayin zantawar tasu a jiya Lahadi, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin hadin kai da Pakistan a fannin karfafa aminci bisa manyan tsare-tsare, da fadada hadin gwiwarsu, da kuma hanzarta gina ingantacciyar makomar al’ummar kasashen biyu ta bai daya.
Wang Yi ya kara da cewa, yanayin da Venezuela ke ciki na janyo hankalin al’ummar kasa da kasa sosai. A ganin Sin, babu wata kasa da ke da ikon tsamo baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasa yadda ta ga dama, kuma bai kamata wata kasa ta zama mai yanke shawara ta kashin kai a harkokin duniya ba, don haka dole ne a mutunta ikon mulki, da tsaron ko wace kasa bisa dokar kasa da kasa. Ya ce ana adawa da amfani da karfi ko barazana a dangantakar kasa da kasa, kuma Sin tana adawa da kakaba tunanin wata kasa kan wasu. Kazalika, Sin tana fatan hada kai da al’ummar kasa da kasa ciki har da Pakistan, don kare kundin mulkin MMD bisa karfinsu.
A nasa bangare, Dar ya jaddada cewa, Pakistan ta sake jaddada rike ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya”, za ta ci gaba da goyon bayan Sin a duk batutuwan da suka shafi muradunta na tushe. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link