Ana zargin ɗan haya da kashe mai gidansa a Gombe
[ad_1]
Al’ummar Unguwar Arawa ta Gabas da ke cikin birnin Gombe sun wayi gari cikin firgici da tashin hankali a safiyar wannan Talatar, sakamakon wani mummunan kisan gilla da ake zargin wani ɗan haya ya aikata kan mai gidansa, wata mata mai suna Maryam Hassan.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa marigayiyar ita ce mamallakiyar gidan da wanda ake zargi da aikata kisan ke zaune a matsayin ɗan haya.
An tsinci gawar Maryam Hassan cikin wani hali mai matuƙar tayar da hankali, lamarin da ya girgiza mazauna unguwar tare da jefa su cikin tsoro da alhini.
Majiyoyi daga cikin unguwar sun bayyana cewa tun kafin faruwar wannan lamari, ana fama da yawan sabani tsakanin marigayiyar da matar ɗan hayar, rikice-rikicen da suka daɗe suna faruwa ba tare da an san ainihin musabbabinsu ba.
Rahotanni sun nuna cewa sabanin ya kai matakin da matar ɗan hayar ta bar gidan, bayan da mijinta ya tura ta zuwa gidansu sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninsu.
Wata majiya daga unguwar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa matar ɗan hayar da marigayiyar na yawan samun sabani, duk da cewa ba a san takamaiman dalilin rikicin ba.
Sai dai majiyoyi sun rabu wajen bayyana wanda ya aikata kisan, yayin da wasu na zargin matar ɗan hayar ce ta shirya a kashe marigayiyar ta hannun wasu mutane da daddare, wasu kuma na zargin cewa shi kansa ɗan hayar ne ya aikata kisan.
Wata majiya ta ce ana zargin ɗan hayar ya tura matarsa ta koma gidansu da hujjar cewa zai yi tafiya, amma daga baya aka gano bai je ko’ina ba.
Majiyar ta kara da cewa bayan matar ta tafi, marigayiyar Maryam Hassan ta kira matar ɗan hayar ta sanar da ita cewa mijinta bai yi tafiya ba kamar yadda ya faɗa mata.
Wannan bayani ne ya sa ake zargin ɗan hayar ya sake tilasta wa matarsa barin gidan gaba ɗaya.
Majiyar ta ce ana hasashen ɗan hayar ya shirya komai ne domin aikata kisan ba tare da matar sa ta sani ba, musamman ganin cewa marigayiyar ta tona masa asiri a wajen matarsa, lamarin da ka iya haddasa masa matsala a gidansa.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da samun rahoton faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun kwashe gawar marigayiyar domin gudanar da bincike.
Ya ce rundunar za ta fitar da cikakken bayani bayan kammala bincike, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu karin bayani daga ‘yan sanda ba.
Tuni aka gudanar da jana’izar marigayiya Maryam Hassan da misalin karfe 2:00 na rana a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, cikin yanayi na jimami da alhini daga ‘yan uwa da al’ummar gari.
Lamarin ya bar tambayoyi masu yawa a zukatan jama’a, yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon binciken jami’an tsaro domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma hukunta wanda aka samu da laifi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link