Manyan Jami’o’in Kasar Sin Sun Samar Da Karin Guraben Karatu 38,000 Cikin Shekaru Biyu Da Suka Gabata
[ad_1]
Ministan ma’aikatar ilimi na kasar Sin Huai Jinpeng, ya ce manyan jami’o’in kasar Sin sun samar da karin guraben daukar dalibai har 38,000 cikin shekaru biyu da suka gabata.
Huai Jinpeng, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Asabar din nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana yanzu haka, ya ce a cikin shekarun biyu, an samar da sabbin tsare-tsaren hadin gwiwa 540, tsakanin cibiyoyin ilimi, da kwasa-kwasai na babban yankin Sin da sauran kasashe da yankunan duniya daban daban, musamman a matakin digirin farko da matakai na sama da hakan.
Kazalika, ministan ya ce kasar Sin ta kaddamar da manufar yin hutun mintuna 15 tsakanin darussa, da motsa jiki na sa’o’i biyu a kowace rana ga daliban firamare, da na kananan makarantun sakandare, dake dukkanin yankuna na matakin lardi.
Minista Huai ya kara da cewa, alkaluman nazari da mahukuntan kasar suka samu, sun nuna karuwar dukkanin yanayin kiwon lafiyar jikin daliban kasar bisa daidaito, yayin da larurar gaza gani daga nesa ta ragu, tsakanin dalibai cikin shekaru hudu a jere.
A daya bangaren kuma, a shekarar 2025 da ta gabata, adadin daliban kasar Sin da suka shiga manyan makarantun sakandare ya kai kaso 92 bisa dari, karuwar da ta kai kaso 7 bisa 100, idan an kwatanta da alkaluman shekarar 2012. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link