Darussa Daga Ramadan Na 14: Yawaita Kyauta Da Ihsani A Ramalana

[ad_1]

A cikin watan Ramalana muna koyon yawaita kyauta ga mutane, domin wannan wata ne da Allah Maɗaukaki Yake riɓanya ladan kyawawan ayyuka a cikinsa. Idan Ubangiji Yana ƙara lada, ya dace mu ƙara aiki. Idan rahama tana yalwatuwa, to ya dace mu yalwata alheri.

Ramalana wata ne na karamci, karamcin Allah ga bayinsa, da kuma karamcin bayinsa ga junansu. Saboda haka, mumini yana ƙoƙarin riɓanya kyautatawa ibada ga Allah da ciyar da mai azumi, ya taimaki mabuƙata, ya faranta ran marasa ƙarfi, ya kuma shimfiɗa hannu da zuciya ga al’umma. An ruwaito a cikin Sahihul Bukhari cewa: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma ya fi kasancewa mafi yawan kyauta a watan Ramalana” Malaman hadisi sun bayyana cewa kyautar Annabi (S.A.W) a Ramalana ta fi gudun iska mai kaɗawa, watau tana isa ga kowa ba tare da wariya ba.

  • Darussa Daga Ramadan Na 13: Tsayuwar Dare
  • Darussa Daga Ramadan Na 12: Ƙarfafa Alaƙa Da Alƙur’ani A Ramalana

Wannan yana nuna mana cewa Ramalana ba wai kawai wata ne na tsayuwar dare da azumi ba, har ma wata ne na buɗa hannu da yalwar alheri ga mutane. Kyauta ba kuɗi kaɗai ba ce. Akwai kyautar murmushi, da kyautar kalma mai daɗi, da kyautar yafiya, da kyautar taimakon jiki, da kyautar ilimi. Duk abin da ka bayar domin Allah, komai ƙanƙantarsa, to yana da girma a wurinsa Subhanahu wata’ala.

Yawaita kyauta a Ramalana yana gina halaye masu kyau a zuciya kamar:

1. Yana kawar da rowa.
2. Yana raba zuciya daga son kai.
3. Yana ƙarfafa zumunci da haɗin kai.
4. Yana jawo rahamar Allah.

Domin wanda ya yi rahama ga bayin Allah, to Allah zai yi masa rahama. Wanda ya sauƙaƙa wa wani wahala, Allah zai sauƙaƙa masa al’amura.

Ramalana yana koya mana cewa duk abin da muke bayarwa ba ya raguwa; a maimakon haka, yana ninkuwa ne. Domin Allah Mai yalwa ne, kuma Yana saka wa bayi da alheri mai yawa bisa aiki kaɗan da suka aikata.

Idan muka fita daga Ramalana da zuciya mai bayarwa, to mun fahimci darasinsa. Domin al’umma mai karimci ita ce al’umma mai albarka.

Allah Ya sanya mu cikin masu ihsani, Ya wadata mu da zuciya mai yalwatawa bayin Allah, Ya kuma karɓi dukkan abin da muka bayar domin neman yardarsa. Amin.

Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *