’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace malami da wasu 7 a ƙauyen Sakkwato
[ad_1]
Aƙalla mutum huɗu ne suka rasu, yayin da aka yi awon gaba da wasu mutum takwas, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Dudu Barade a Jihar Sakkwato.
Sun kai harin ne a daren ranar Alhamis a ƙauyen da ke Ƙaramar Hukumar Rabah.
Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun shiga da misalin ƙarfe 11:30 na dare sannan suka fara harbe-harbe.
Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce waɗanda aka kashe sun haɗa da maza uku da mace ɗaya.
Ya bayyana sunayensu; Suleiman Dahiru, Naziru Abubakar, Isah Abubakar da Wakala Muhammad.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wani malami da mata shida, ciki har da matar malamin da kuma jariri.
“Waɗanda aka sace sun haɗa da Malam Dahiru Lawwali, Safiya Malam Dahiru, Asmau Abubakar, Ubaida Ibrahim, Rakiya Yakubu, Nafisa Aliyu da kuma wani jariri da ba a san sunansa ba,” in ji shi.
Majiyar ta ce ’yan sa-kai na ƙauyen sun yi ƙoƙarin yin artabu da maharan, amma ba su yi nasara ba.
“’Yan sa-kai sun gwabza faɗa da ’yan bindigar, amma maharan sun fi su ƙarfi,” in ji shi.
Mazauna yankin sun kuma nuna damuwa kan rashin isassun jami’an tsaro a ƙauyen, inda suka buƙaci gwamnati ta tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
“Muna cikin wani mawuyacin hali. Da yawa daga cikinmu sun bar ƙauyen domin yin buɗa-baki a wasu wurare, kuma wasu na tsoron kwana a gida saboda fargabar sake kawo wani hari,” in ji majiyar.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, ya ce zai tuntuɓi jami’in yankin domin samun ƙarin bayani.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai yi ƙarin haske ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link