’Yan bindiga sun yi garkuwa da Fulani a Kogi
[ad_1]
Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Jege da ke Karamar Hukumar Yagba ta Gabas da ke Jihar Kogi, inda suka sace wasu mazauna yankin, da ba a kai ga tantance adadinsu ba.
An ce mutane da dama ne aka tafi da su zuwa maboyar miyagun da ke cikin dazukan yankin.
Rahotanni daga yankin a ranar Talata sun bayyana cewa ’yan bindigar kutsa cikin garin ne a tsakar daren Litinin, suna harbe-harbe.
Wani mazaunin garin Ejuku, makwabciyar Jege, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Yanayin tsaro a Jege ya yi matukar munana tun da safiyar yau. Mutane da dama ne aka sace a harin ’yan bindigar a daren Litinin.
“A halin yanzu ba zai yiwu a tantance adadin wadanda aka sace ba. A cikin rudanin da ya lullube al’ummar, mutane da dama sun tsere, wasu kuma har yanzu suna barin garin. Ba mu san wanda ya tsere ba, ko wanda aka sace a yanzu.”
Shugaban Kungiyar Cigaban Jege (JDA), Oluomo JD Akogun, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sada zumuntar al’ummar yankin a daren Litinin, ya ce, “Rahoton da ya zo min shi ne cewa an kai hari wani sansanin Fulani da ke tsakanin Jege da Ejuku.
“Rahotannin harbe-harbe masu yawa sun mamaye garin Jege. An ce wasu daga cikin Fulani ne aka sace a harin da ’yan bindigar suka kai.”
Bincike da aka gudanar a ranar Talata ya nuna cewa fargaba ta mamaye mazauna yankin, inda da dama ke ta faman tuntubar ’yan uwansu da masoyansu domin tabbatar da halin da suke ciki.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, CSP William Aya, bai amsa kiran waya ko sakon tes ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link