Dan ƙunar baƙin wake ya ya kashe sojoji 5 a Borno
[ad_1]
Wani dan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa bam, inda ya halaka sojoji biyar a garin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Mazauna yankin da kuma majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a wani shingen binciken sojoji.
Wata majiya ta ce ana zargin maharin ɗan kungiyar ISWAP ne, wanda ya dade yana buya a tsaunukan Mandara.
Majiyar ta ce, “Wasu sun bayyana cewa ya kwana kusa da shingen sojojin yana shirin aikata wannan mummunan aiki.
“Da safe, lokacin da aka buɗe hanya ga masu wucewa, sai ya yi kamar ɗaya daga cikinsu, ya tayar da bam a cikinsu. Sojoji biyar suka rasa rayukansu nan take.”
Wani mazaunin yankin ya ce, “Tun fiye da shekara guda kenan, wannan shi ne kawai harin kunar bakin wake da aka samu a nan. Wannan na nuni da bukatar sabuwar dabarar jami’an tsaro don kauce wa maimaituwar hakan.”
Wannan sabon hari ya tunatar da munanan tarihin hare-haren kunar bakin wake da aka taba kai wa a Gwoza da sauran sassan jihar ta Borno.
Ko a ranar 30 ga watan Yunin 2024, wasu mata biyu ’yan kunar bakin wake sun tayar da bama-bamai a wajen bikin aure a garin Gwoza, inda suka kashe mutane 18 ciki har da yara da wata mace mai juna biyu.
Haka kuma, a ranar 21 ga watan Yuni, 2025, akalla fararen hula 11 suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wajen kallon wasan kwaikwayo a karamar hukumar Konduga.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link