Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Umarci Shugabannin Tsaro Su Koma Maiduguri

[ad_1]

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci shugabannin rundunonin tsaro su koma Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin su jagoranci magance matsalar tsaro a can.
Wannan na zuwa ne bayan hare-haren bama-bamai da dama da suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20 tare da jikkata sama da mutane 100.
A jiya daren Litinin, mun rahoto muku yadda wasu jerin fashe-fashen bama-bamai suka faru a jihar, inda ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai hare-hare a lokaci guda da misalin ƙarfe 7:25.
Da yake mayar da martani kan wannan mummunan lamari kafin ya tashi zuwa ziyarar aiki mai tarihi zuwa birnin Landan, Tinubu ya ce Nijeriya ba za ta mika wuya ga tsoron ‘yan ta’adda ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *