Yara 48 aka sace tare da kai su Kudu — Gwamnan Gombe
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan sace yara 48 ’yan asalin jihar masu shekaru tsakanin biyu zuwa biyar.
Gwamnan ya bayyana haka a wani taro a Gombe, inda ya ce ana zargin an kai wasu daga cikin yaran zuwa Kudancin Najeriya.
Ya ce har yanzu ba a san halin da yaran suke ciki ba, kuma gwamnati na ci gaba da bincike tare da haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin gano su.
Gwamnan ya jaddada cewa tsaro alhakin kowa da kowa ne, ba iya gwamnati kaɗai ba.
Ya roƙi jama’a su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai domin taimakawa wajen gano yaran da hana irin wannan faruwa a nan gaba.
Haka kuma, ya ce gwamnati ta ɗauki matakai kamar hana cinikin ƙarafa da kuma taƙaita zirga-zirgar babura a wasu wurare domin rage laifuka.
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da ƙoƙarin ganin an ceto yaran lafiya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link