Atiku ya soki tafiyar Tinubu Birtaniya ana tsaka da alhinin harin Maiduguri
[ad_1]
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki tafiyar shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa Birtaniya, a daidai lokacin da aka kashe mutane a harin ta’addanci a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa, Atiku ya bayyana baƙin ciki kan harin, yana mai cewa bai dace shugaban na Najeriya ya fice daga ƙasar ba yayin da ake alhinin mutuwar jama’a.
Ya zargi gwamnatin da rashin bai wa tsaron jama’a fifiko, yana mai cewa sojoji na fuskantar ƙalubale na tsoffin makamai, yayin da hare-haren ta’addanci ke ci gaba da ƙara tsananta.
Atiku ya kuma ce, ya kamata Sarki Charles III wanda Tinubu zai kaiwa ziyara ya san halin da Najeriya ke ciki, inda a cewarsa ana binne waɗanda aka kashe, yayin da shugaban ƙasa ke gudanar da ziyarar aiki a ƙasarsa.
Ya ƙara da cewa, duk da umarnin da aka bai wa jami’an tsaro, hare-haren ‘yan ƙunar baƙin wake na ci gaba, yana mai cewa hakan ya nuna akwai buƙatar sake duba dabarun yaƙi da ta’addanci.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi gwamnatin da mayar da sukar ta a matsayin cin amanar ƙasa, yana mai cewa hakan na hana a yi gyara mai ma’ana.
Atiku ya shaida wa gwamnati mai ci cewar ba za ta yi kamfen na zaɓen shekarar 2027 a kan kaburburan jama’a ba, waɗanda ta gaza kare rayukan su, inda ya nanata buƙatar gwamnati ta mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Duk da sukar da ya yi, Atiku ya jinjina wa jami’an tsaro da ke sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link