Makiyayi ya kashe dansa mai shekara 11 a wajen kiwo

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta kama wani makiyayi mai suna Jatau Jaye, saboda zarginsa da kashe dan cikinsa mai shekara 11 mai suna Buhari a jihar Kogi.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kauyen Agbaja na karamar hukumar Oworo da ke jihar, lokacin da mahaifin ya tafi kiwo da dan nasa ranar 19 ga watan Agusta amma bai dawo gida ba.

Mahaifiyar yaron mai suna Adama ce ta ce ba ta ga dan nata ba tun bayan fitarsu tare da mijinta, lamarin da ya sa aka bazama nemansa a cikin daji, kafin daga bisani a gano gawarsa.

Adama ta ce lokacin da aka ga gawar yaron, an ga mahaifin nasa a wajen yana kokarin binne shi saboda kada a gane shi ya kashe shi.

Jami’an ’yan sanda daga Lokoja sun bazama wajen inda suka dauki bayanai sannan suka kama wanda ake zargin.

Daga bisani kuma ’yan sanda sun ba iyalan mamacin gawar, inda aka yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Lokacin da aka titsiye makiyayin, ya amsa cewa shi ne ya kashe dan nasa ta hanyar dukansa da sandar kiwo, saboda wani laifi da ya yi masa lokacin da suke tsaka da kiwon.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *