2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya.

Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba.

Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, sai ya ce lokacin tattauna hakan bai yi ba.

Ya ce, “Lokacin hakan bai yi ba tukuna. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yana da amfani ga kasa.

“In har matashi ya kayar da ni, zan amince da sakamakon kuma in mara masa baya da dukkan zuciyata, in kuma ba shi shawarwari. Jam’iyyarmu tana samun karbuwa,” in ji Atiku.

Ya ƙara da cewa babban abin da ya fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne karfafa kawancen haɗakar ADC.

“Jam’iyyarmu tana ba matasa da mata muhimmanci. Wannan shi ne babban burinmu,” in ji shi.

Atiku ya bukaci matasa da su shiga harkar siyasa da kuma neman mukaman siyasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *