An biya wa tsuntsaye kuɗin kujerun jirgin sama
Wasu kamfanonin jiragen sama na Gabas ta Tsakiya suna barin shaho (falcons) su yi tafiya a cikin gida, galibi suna buƙatar su sami tikitin kansu da takardun yin balaguro a jirgi.
Wani matafiyi ɗan ƙasar Jamus mai suna Tom, kwanan nan ya haɗu da wani abu da ba kasafai ake gani ba a cikin wani jirgin saman ’yan kasuwa a Gabas ta Tsakiya, inda gaba ɗayan jerin wani sashen kujerun fasinjoji na ɗauke da shahonni (fulcons) wanda suke zaune cikin kwanciyar hankali a cikin jirgin ɓangaren fasinjoji.
Tom ya ɗauki ɗan gajeren bidiyo da ke nuna shahonni da yawa da ke zaune kan kujerun fasinja, duk sun yi shiru cikin natsuwa. Tsuntsayen suna sanye da abu mai siffar huluna don su sami nutsuwa yayin tafiya.
Wannan sananniyar al’ada ce a ƙasashen Larabawa na yankin Gulf, kodayake ya kasance abin ban mamaki ga mutane daga sassan duniya. Mutumin ya lura a cikin taken saƙon da ya wallafa, wannan kawai zai iya kasancewa a cikin ƙasashen Larabawa” kamar Qatar da Daular Larabawa ta UAE da Oman da Saudiyya, inda shaho ya kasance muhimmin ɓangare na al’adun gargajiya.
‘’A ina ne a duniya wannan zai iya faruwa? Sai dai a yankunan Larabawa. Na tabbata ana biyan tikitin shahon, kamar yadda aka ɗauki hoton bidiyon a Instagram’’, a cewar Tom.
Bidiyon ya karaɗe shafukan intanet, inda ya ɗauki hankalin Mabiya shafukan, inda ya haifar da ra’ayoyi daban-daban, da suka haɗa da nishaɗi da masu son abubuwan buɗe ido da bambance-bambancen al’adu da son walwalar dabbobi. Wasu kamfanonin jiragen sama na Gabas ta Tsakiya suna barin shaho (falcons) su yi tafiya a cikin gida, galibi suna buƙatar su sami tikitin kansu da takardun balaguro.
Wani mai amfani da shafin ya rubuta, “ba abin mamaki ba ne, waɗannan shahonni suna da ma’ana mai zurfi a cikin al’adunsu. Abubuwan sukan faru, akwai wasan gasar da akan yi a can.
Na ga yadda ake jigilar tsuntsayen a jiragensu sau da yawa, ana kula da su a hankali da tsaro, saboda suna da daraja mai yawa.”
Wani kuma ya ce, “Shin suna da fasfo? Idan haka ne, na yi amanar fasfoɗinsu ya fi fasfona.”
A nemi Jaridar AMINIYA don samun karin bayani.