Sin Ta Bayyana Taron Shawarwarinta Da AU A Matsayin Muhimmin Mataki Na Cudanya Bayan Kama Aikin Kwamitin AU
[ad_1]
Jiya Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, Mahmoud Ali Youssouf, sun yi shawarwari kan manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da kungiyar AU karo na 9 a hedkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha. Game da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, shawarwarin da aka yi muhimmin mataki ne na yin cudanya tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare, tun bayan sabon kwamitin kungiyar ya fara aiki.
Hakazalika kakakin ta jaddada cewa, kasar Sin na son yin aiki tare da kungiyar AU don tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin shawarwarin, tare kuma da fadada fannonin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, don kara amfanar da jama’ar kasar Sin da na kasashen Afirka.
Har ila yau, an kaddamar da shekarar cudanyar jama’a da musayar al’adu a tsakanin Sin da Afirka ta shekarar 2026 a jiya a hedkwatar kungiyar ta AU. A yayin da take karin bayani game da batun, kakakin ta ce, a shekarar nan da muke ciki bangarorin Sin da Afirka za su gudanar da kusan harkokin musayar al’adu har kusan 600 bisa taken “Ƙarfafa zumunci ko yaushe daga dukkan fannoni, da hada karfi da karfe wajen cimma burin zamanantarwa”. (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link