Tinubu ya amince da tura jakadu 65 zuwa ƙasashe daban-daban
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadu 65 domin wakiltar Najeriya a ƙasashe daban-daban da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce daga cikin jakadun, 34 ’yan siyasa ne, yayin da 31 kuma ƙwararrun jami’an diflomasiyya ne daga ma’aikatar harkokin waje.
Daga cikin manyan waɗanda aka naɗa akwai tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode wanda aka tura zuwa Jamus, yayin da mai taimaka wa shugaban ƙasa Reno Omokori zai wakilci Najeriya a ƙasar Mexico.
Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau kuma zai je ƙasar China, yayin da Sanata Jimoh Ibrahim zai wakilci Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu wanda aka tura zuwa Spain, da tsohon Ministan Lafiya, Isaac Adewole wanda zai yi aiki a ƙasar Kanada.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce wasu ƙasashe sun riga sun amince domin karɓar jakadun.
Haka kuma an aike buƙatar irin wannan amincewa ga sauran ƙasashen da za a tura jakadu.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da sunayen jakadun a watan Disamban 2025.
Ana sa ran za su fara aikinsu ne bayan sun kammala shirin ɗaukar horo na musamman da kuma samun cikakkiyar amincewa daga ƙasashen da za su je.
Najeriya na da ofisoshin jakadanci a sama da ƙasashe 100 a duniya.
Waɗannan ofisoshi na taimakawa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashe, bunƙasa kasuwanci, da kare muradun Najeriya a ƙasashen waje.
Lokaci na ƙarshe da aka tura jakadu da yawa shi ne a shekarar 2017, lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Hakan ya sanya wasu ofisoshin jakadancin Najeriya suka daɗe ba tare da waɗanda za su jagorance su ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link