’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i da sauran jagororin jam’iyyar ADC kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye.

A cewar takardar wacce Aminiya ta gani, an gayyace su ne domin su yi wa rundunar bayani kan zargin su da hadin baki da tunzura jama’a wajen tayar da tarzoma da kawo wa zaman lafiya tarnaki a jihar.

Takardar, wacce ke dauke da kwanan watan hudu ga watan Satumban 2025 dai na dauke ne da sa hannun Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (SCID), Uzairu Abdullahi.

Takardar ta ce, “Wannan sashen namu na bincike a kan wadannan tuhume-tuhumen da ya kunshi ’yan jam’iyyarka. Ana bukatar ka zo tare da su zuwa rundunarnu ranar takwas ga watan Satumba domin ku yi bayani kan zarge-zargen da ake yi muku.

“Wadanda ake gayyatar su ne: Mal. Nasir El-Rufa’i, Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed (30), Nasiru Maikano, Aminu Abita da kuma Ahmed Rufa’i Hussaini (Mikiya).”

Da wakilinmu ya tuntubi mataimakin shugaban ADC na kasa shiyyar Arewa maso Yamma, Jafaru Sani, wanda shi ma sunansa na cikin wadanda ake gayyatar, ya ce, galibinsu su ma a kafafen sada zumunta na zamani suka ga labarin gayyatar.

“Haka ne, amma galibinmu ma a kafafen sada zumunta muka ga labarin gayyatar,” in ji Jafarun, yayin da ya ki yin wani karin haske a kan hakan.

A makon da ya gabata ne aka yi musayar yawu tsakanin Gwamnatin Kaduna da tsohon Gwamnan kan wasu ’yan daba da suka kai wa taron jam’aiyyar ADC hari a Kaduna, sannan suka jikkata wasu mahalarta taron.

El-Rufa’is dai ya zargi gwamnatin jihar da aike musu da ’yan dabar a matsayinsu na ’yan adawa, amma ita kuma gwamnatin ta musantanta kuma ce El-Rufa’in ne da kansa ya dauki nauyin hargitsa taron don kawar da tunanin mutane.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *