Mutane 21 Sun Mutu, Wasu 30 Sun Jikkata A Hatsarin Jiragen Ƙasa Biyu A Kudancin Andalus

[ad_1]

Aƙalla mutane 21 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon hatsarin karo tsakanin jiragen ƙasa biyu a kudancin ƙasar Spain a daren Lahadi, kamar yadda hukumomin ƙasar suka tabbatar. Lamarin ya jefa al’umma cikin jimami, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da ƙoƙarin taimakon waɗanda suka jikkata a wurin hatsarin.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na dare a kusa da garin Adamuz, a lardin Cordoba. Rahotanni sun ce jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinjoji kusan 300 daga Malaga zuwa Madrid ne ya yi karo da wani jirgi da ke kan hanyarsa daga Madrid zuwa Huelva, wanda ke ɗauke da kimanin fasinjoji 200, a cewar hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar, ADIF.

  • Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing
  • Ingila Da Spain Wa Zai Yi Nasara A Berlin?

Ministan Sufuri na ƙasar, Oscar Puente, ya bayyana cewa har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba, yana mai cewa abin ya kasance “abin mamaki matuƙa,” ganin cewa hatsarin ya auku ne a kan madaidaicin layin dogo, inda ya kamata a samu cikakken tsaro da kulawa.

A martaninsa, Firayim Ministan Spain, Pedro Sanchez, ya bayyana lamarin a matsayin babbar musiba ga ƙasar baki ɗaya, tare da bayar da umarnin dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa tsakanin yankin Andalusia da birnin Madrid na wani lokaci, domin bai wa jami’an tsaro da masu bincike damar tantance ainihin abin da ya jawo hatsarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *