An Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Ƙunar Baƙin Wake A Masallacin Borno

[ad_1]

Sojojin Operation Hadin Kai sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu kan harin kunar bakin wake na baya-bayan nan a wani masallaci a Maiduguri, Jihar Borno.

Wannan ya zo ne kwana uku kacal bayan da sojoji suka kama shugaban dake jagorantar shirin kai harin, mai suna Sheriff Umar, a babban birnin jihar.

Mun rahoto muku cewa, harin kunar bakin waken ya faru ne a ranar 24 ga Disamba, 2025, a cikin wani masallaci a Kasuwar Gamboru, Maiduguri, wanda ya kashe akalla masu ibada biyar tare da jikkata wasu 35.

A cikin wata sanarwa, Jami’in Yada Labarai na Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya ce an kama mutanen ne a lokacin wani bincike da aka yi a yankin ‘Yan Lemu da ke karamar hukumar Mubi ta Kudu a jihar Adamawa

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *