Sallah: Gwamnan Gombe ya buƙaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya buƙaci Musulmi da duk ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a da kuma riƙe darusan da suka koya a watan Ramadan yayin bikin ƙaramar Sallah.
A sakon taya murna da ya fitar, gwamnan ya ce bai kamata a ɗauki Sallah a matsayin shagali kawai ba, ya buƙaci yi amfani da darusan da aka kowa a Ramadan a rayuwar yau da kullum.
Ya ce halaye irin tsoron Allah, biyayya da sadaukar da kai ya kamata su ɗora a rayuwar jama’a.
“Mu yi amfani da darusan Ramadan wajen inganta zaman lafiya, juriya da soyayya a tsakaninmu,” in ji shi.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubale.
Ya kuma buƙaci ’yan kasa da kada su yanke ƙauna, su haɗa kai tare da ƙarfafa imaninsu.
Gwamnan ya roƙi al’ummar Gombe da su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa zaman lafiya shi ne tushen ci gaba.
Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo tashin hankali ba.
Har ila yau, gwamnan ya gode wa jama’a bisa goyon baya, ya kuma taya Musulmi murnar Sallah tare da yi musu fatan farin ciki da kwanciyar hankali.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link