Yadda Tsare-tsaren Tinubu Na Fitar Da Kaya Ketare Suka Ƙara Wa NPA Ƙwarin Guiwa

[ad_1]

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta fitar da wata gagarumar nasara da ta samu, tun daga shekaru baya.

Wannan gagarumar nasarar ta Hukumar shi ne, yadda biyo bayan tsare-tsaren da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samar, hakan ya karawa NPA kwarin guiwar, iya fitar da Kwantainoni zuwa kasar waje, da yawan su ya kai kaso 1,085.

  • ICPC Za Ta Ci Gaba Da Binciken Tsohon Shugaban NMDPRA Duk Da Janye Ƙarar Dangote
  • Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi

Kazalaika, hakan ya kuma sanya,  a zango na uku na shekarar 2025, yawan Kwantainonin daga a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka  karu yawan jimlar metric tan 33.52.

Bisa wasu alkaluma da Hukumar ta NPA ta fitar a ranar Litinin da ta gabata a babban birnin tarayyar Abuja, sun nuna cewa, duk a shekarar ta 2025, Jiragen Ruwan da suka fita daga Tashoshin Jiragen Ruwan kasar sun karu, daga kaso 16.2 zuwa kaso metric tan miliyan 28.84,  wanda hakan ya nuna cewa, sun kai kusan adadin Jiragen Ruwan da suka fita daga kasar a zango na uku na shekarar 2024.

Bugu da kari, hakan ya kuma irin yawan adadin hada-hadar ayyukan da aka gudanar a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.

Hakazalika, an dai danganta irin wannan kokarin, bisa sauye-sauyen kara habaka tattalin arzikin kasar da Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta kirkiro da su, musamman domin a samar da sauki, wajen fitar da kayan da basu shafi Man Fetur ba, daga cikin kasar nan, zuwa waje.

Wasu daga cikin masu fashin baki kan wadannan sauye-sauyen da da Gwamnatin ta samar, sun kara karfafa guiwar masu zuba jari, a kasar musamman a bangaren harkar sufurin Jiragen Ruwan kasar, duba da cewa, fannin ya kasance, wani babban ginshiki, wajen kara habaka tattalin arzikin kasar.

Hada-hadar ayyukan safarar Kwantaina, na kara taka gagarumar rawa, wajen kara bunkasa fannnin sufurin Jiragen Ruwa.

Bugu da kari, a zango na uku na shekarar 2025, ta karu daga kaso 18.9 zuwa kaso 546,931, idan aka kwatanta da wanda aka yi, a zango na uku na shekarar 2024, wanda ta karu zuwa kaso 460,038.

Bisa wannan yan Kwantainar da suka shigo cikin kasar nan, sun karu daga kaso  33.1 zuwa kaso 268,713 da kuma kara samun wata karuwar da ta kai kaso 201,839, a shekarar ta 2025.

Bugu da kari,  Kwantainar da aka fitar sun karu zuwa kaso 69,039 daga kaso 5,812, duk a shekarar ta 2024.

Karin samun fitar da Kwantainar, ya haifar da raguwar fitar da Kwantainonin da babu komai a cikinsu, zuwa  kaso 21.5.

Hakazalika, an kara samun yawan Jiragen Ruwan da suka fita daga kasar a zango na na uku, na shekarar 2025, inda kuma wasu suka karu daga kaso 8.4 zuwa kaso 1,074, haka an kara kuma samun wata karuwar ta fitar Jiragen a zango na uku, na shekarar 2024, da suka kai kaso 991.

Bugu da kari, yawan rijista ta GRT ta karu daga miliyan 18 zuwa miliyan 42.64, idan aka kwatanta da miliyan 36.13 da aka samu a shekarar.

Bisa adadin wadannan Jiragen Ruwan da suka fita daga kasar, Tashar Jiregn Ruwa ta Tin Can, ta kasance, ita ce a kan gaba wadda keda kaso 22.7, sai kuma Tashar Apapa, da ke bita mata wata take da kaso 22.2.

Kazalka, Tashar Onne da kuma ta Lekki, inda ta Onne ta kai kaso 18.9 sai kuma ta Lekki, da ta kai kaso18.4, inda kuma ta Kalaba, ta kai akalla kaso 2.1.

Bugu da kari, Jiragen Ruwa da suka sauka a Tashar Lekki, wadanda kuma aka uiwa rijista, sun kai yawan  57,244,  inda kuma wadanda suka sauka a Tashsar Onne, suka kai yawan  51,276.

Su kuwa Tashar Apapa Jiragen Ruwa da suka sauka sun kai 35,556, inda kuma a ta Tin Can, suka kai  34,400 sai kuma a ta da suka kai tan  18,677 duk a zango na uku, na shekarar ta 2025.

Tashar Onne, ta samar da kaso 17,  sai kuma Tashar Apapa da ke da kaso 15.1, inda kuma Tashar Tin Can Island, ke da kaso 10, inda kuma Tashar Kalaba, ita ma ta samu kaso kasa da haka.

Bisa fashin bakin da aka yin a yawan kayan sun nuna cewa, sun karu zuwa kaso 53.8, inda kuma yawan Kwantainar da Jiragen Ruwan suka yo jigilar su, suka kai kaso 26.6, inda kuma a Tashar Jiragen Ruwa na kan Tudu, suka kai kaso  11.3 da kuma sauran da suka kai kaso 8.2.

Da yake yin tsokaci kan wadannan alkaluman, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, ya dantanta wannan gaguwar nasarar da aka samu, bisa sauye-sauyen kara bunkasa tattalin azirkin kasar, da Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta kirkiro da su.

Kazalika, Dantsoho ya kara da cewa,  jagorancin Minitsan Bunkasa Fannin Tattalin Arziki na Teku Adegboyega Oyetola, hakan ya kara taimaka wa, wajen kara samun wannan nasarar a shekarar ta 2025.

Bugu da kari, ya sanar da cewa, kara karfafa fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar ya kara kwarin guiwa  ga fannin na sufurin Jiragen Ruwa na kasar.

Shugaban ya ci gaba da cewa,  bisa irin kyawawan zamanantar da fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar wanda Ma’aikatar Bunkasa Tattlin Arziki na Teku musamman ta hanyar yin amfani da tsarin na’urar truck call-up system, hakan ya kara sanya an samu sauki a fannin, musamman wajen gudanar da sufurin Jiragen Ruwa a tsakanin yankunan kasashe, anda hakan ya kara habaka gudar da hada-hadar kasuwanci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *