Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Furucin Trump Na “Ba Na Bukatar Dokokin Duniya” Yana Fayyace Gaggauta Gyara Jagorancin Duniya Ne
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa “Ba na bukatar dokokin duniya”, a wata hira da ya yi da jaridar New York Times kwanan nan, ’yan kwanaki kadan bayan harin da sojojin Amurka suka kai wa Venezuela da kuma tsare shugaba Nicolas Maduro ta hanyar tilastawa. Wannan bayanin ya nuna cikakken kudurin Amurka na yin gaban kanta da kuma turbar da ta dauka ta yin babakere. Jaridar New York Times ta lura cewa, abin da Trump ya kwatanta da ’yancinsa na amfani da duk wani abu da ya shafi karfin soja, tattalin arziki ko siyasa don karfafa Amurka ta danne kowa, shi ne babbar shaidar da ke nuna ra’ayinsa na yin abin da ya ga dama a fagen duniya.
A wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar a duniya, kashi 93.5 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa Amurka, ta hanyar yin gaban kanta, ta mayar da kanta a matsayin ’yar adawa ga al’ummar kasa da kasa. Haka kuma, kashi 91.7 cikin dari na mutanen na ganin cewa gyara tsarin jagorancin duniya wani muhimmin abu ne da ke bukatar ba shi fifiko cikin gaggawa.
An gudanar da wannan kuri’ar jin ra’yoyi ce a sassan shafukan CGTN na harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, inda aka ji ra’ayoyi daga masu amfani da shafukan intanet kimanin 24,000 a cikin sa’o’i 24. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link