Matar da ta haifi jarirai 5 a Kano ta rasu

[ad_1]



Matar da ta haifi jarirai biyar a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, Hafsat Yusuf, ta rasu.

Mijinta, Salisu Nafiu ne, ya tabbatar da rasuwarta, inda ya ce ta rasu a asibitin da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Alhamis.

“Dukkanin jariran guda biyar; maza uku da mata biyu, suna raye kuma suna samun kulawar likitoci,” in ji shi.

Hafsat ta haihu ne bayan an yi mata tiyata a ranar Laraba da rana.

Tun da farko, mijinta ya bayyana farin cikinsa kan nasarar haihuwar, inda ya ce wannan ce haihuwarta ta tara.

Ya kuma ce ma’aikatan lafiya suna bai wa jariran kulawa ta musamman domin tabbatar da lafiyarsu.

Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da cewa za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar jariran gaba ɗaya.

Jami’an gwamnati sun ce hakan na daga cikin ƙoƙarin inganta lafiyar uwa da jarirai da kuma rage mace-macen mata yayin haihuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *