Kotu Ta Ɗaure Iyaye Biyu Kan Safarar Ƴaƴansu Da Wasu Yara A Ribas
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kalaba ta yanke hukuncin ɗauri kan wasu maza biyu bayan an same su da laifin safarar yara takwas ciki har da nasu ƴaƴan.
Waɗanda aka yanke wa hukunci su ne Mabum Arisha da Mutashu Mabum daga Mfom 1 a Ogoja. Mai shari’a L. Ojukwu ya tabbatar da laifinsu a kan tuhume-tuhume 17 baki ɗaya.
- Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
- Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Ribas
Kotun ta ji cewa sun miƙa yaran ga wata Ada Eze domin cin zarafi yara. An ce har yanzu waccan matar ta tsere, yayin da aka kama mutanen biyu.
An shigar da ƙarar ne tun 16 ga Agusta, 2024 kuma aka gurfanar da su 17 ga Oktoba, 2024. Duk da sun musanta laifin da farko, kotu ta same su da laifi bayan kammala shari’a.
An yanke wa Arisha ɗaurin shekaru 12 tare da zaɓin tarar Naira miliyan 2 a kowanne laifi. Haka kuma Mabum ya samu irin wannan hukunci tare da zaman gidan yari a lokaci guda.
Kotun ta kuma umarci a kula da wata yarinya da aka ceto mai suna Favour Arisha. Za ta kasance ƙarƙashin gwamnatin Cross River ta hannun ma’aikatar jin daɗin jama’a.